IQNA

An Tarjama Fim Din Tarihin Manzon Allah Da Yaruka Uku

15:53 - May 27, 2009
Lambar Labari: 1783983
Bangaren kasa da kasa: An tarjama fim din nan na tarihin manzon Allah mai suna manzon rahma SAW zuwa yaruka fitattu na duniya, wato harsunan larabci da kuma turanci gami da faransanci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Alwatan ta kasar saudiyya cewa; An tarjama fim din nan na tarihin manzon Allah mai suna manzon rahma SAW zuwa yaruka fitattu na duniya, wato harsunan larabci da kuma turanci gami da faransanci. Babban sakataren cibiyar kula da yada masaniya tare da wayar da kan al'ummomi kan manzon Allah ta kasa da kasa ya bayyana cewa; babbar manufar samara da wanna fim ita ce bayyana hakikanin tarihin manzon Allah, da kuma irin gwagwarmayar da ya yi wajen yi wa dan adam hidima. Da kuma irin tsarkakan manufofin da ke tattare da sakon da ya zo da shi daga Allah madaukakakin sarki. Wannan zai taimaka matuka wajen wayar da kan wadanda ba musulmi ba su fahimci hakikanin musulunci wanda manzon Allah ya zo da shi, tare da sanin kyawawan dabi'unsu da tausayinsa da 'yan adamtakarsa.

411329


captcha