Bangaren al'adu da fasaha: dakin kula da al'adun Jmahuriyar musulunci ta Iran a Tailand a daidai lokacin tunanawa da cike shekaru ashirin da rasuwar Imam Khomeini® ta ware wani filin nazari kan tunanin Imam Khomeini ® a tarihin musulunci,hadin kai,siyasa da iyali.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce daga yankin kudu maso gabacin Asiya ta watsa rahoton cewa:a wannan taro da za a gudanar a nan gaba a kasar Tailand musamman a garin Bankuk zai yi nazari da binke kan tunani da mahangar Imam Khomeini wanda ya assasa jamhuriyar musulunci ta Iran da kuma yadda tunaninsa a mahangogo da bangarori daban-daban suka taimakawa al'ummar duniya musamman ma al'ummar musulmin duniya.
411357