IQNA

Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi Za Ta Yi Riko Da Matakan Da Ta Yanke

Bangaren siyasa da zamantakewa: ministan harkokin wajen kasar Suriya ne ya bayyanacewa a wajabin day a gabatar ya bukaci kungiyar hadin kan kasashen musulmi da ta jaddada da aiki da alkawulanta.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce daga kasar Suriya ta watsa rahoton cewa: bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta gwamnatin kasar ta Suriya cewa; Walid Mu'allim ministan harkokin wajen kasar ta Suriya a wani zaman manema labarai tare da Ikmalul Dine Ihsan uglu babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ya bayyana cewa kungiyar da hadin kan kasashen musulmi ya kamata ta yi dubi a baya kan ayyukan da ta gudanar a siyasa da tattalin arziki a mataki na kasa da kasa da kuma rawar da ta taka wajen warware matsalolin duniyar musulmi da kareta daga irin wannan matsaloli.

411464