Bangaren kasa da kasa; Ci gaban zamani bai yi karo da manufofin addinin musulunci, amma a lokaci guda musulunci bai amince da karbar gurbatattun al'adu da zamani ke zuwa da sub a, wadanda suka yi hannun riga da koyarwarsa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na yeman news cewa; babban sakataren kungiyar da ke kula da harkokin ilimi ta kasashen musulmi Abdullah bin Abdulmuhsin Al-turki ya bayyana cewa; Ci gaban zamani bai yi karo da manufofin addinin musulunci, amma a lokaci guda musulunci bai amince da karbar gurbatattun al'adu da zamani ke zuwa da sub a, wadanda suka yi hannun riga da koyarwarsa. Alturki ya bayyana hakan ne a wani zama da wakilan kasashen musulmi suka gudanar a birnin San'a na kasar yeman, dangane da yadda ya kamata kasashen musulmi su karbi ci gaban zamani da kuma yin aiki da shi daidai da koyarwar addinin musulunci, tare da yin watsi dab akin dabi'u da suka yi karo da koyarwar ta addinin musulunci.
412134