Bangaren kasa da kasa: A jiya ne aka gudanar da bukin bude sabuwar hanyar karatun kur'ani ta internet a birnin Doha fadar mulkin kasar Qatar, domin sawake wa masu sha'awar koyon karatun kur'ani ba tare da halartar aji ko a gaban malami ba.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jarida kasar Qatar ta Alsharq cewa; A jiya ne aka gudanar da bukin bude sabuwar hanyar karatun kur'ani ta internet a birnin Doha fadar mulkin kasar Qatar, domin sawake wa masu sha'awar koyon karatun kur'ani ba tare da halartar aji ko a gaban malami ba. Babbar cibiyar kula da harkokin kur'ani ta kasar ita ce ta dauki nauyin bude wannan sabuwar hanya, da nufin kara saukaka hanyoyin koyon karatun kur'ani mai tsarki ga dukkanin masu son koyon karatun kur'ani ta wannan hanya, musamman ma matasa daga cikinsu, shugaban cibiyar ya ce da yardarm Allah za su ci gaba da yin dukkanin kokari wajen ganin sun cimma burinsu ta wannan hanya.
412082