Bnagaren kasa da kasa: An gudanar da wani taro day a kebanci mata musulmi a birnin Manglor na jahar Karnaka a kasar India.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Times of India cewa; An gudanar da wani taro day a kebanci mata musulmi a birnin Manglor na jahar Karnaka a kasar India. Rahoton ya ci gaba da cewa daliban jami'a mata ne suka shirya gudanar da wannan taro, da nufin fito da hakikanin matsayin musulunci kan matsayin mace da kimarta a cikin rayuwar zamantakewa, da kuma rawar da za ta iya takawa wajen ciyar da al'umma gaba, gami da wayar da kan wasu dab a su fahimci addinin musulunci ba, wanda hakan ne yasa suke kallon mabiya addinin musulunci a matsayin wasu mabiya addini maras tushe. Wannan taro ya yi dubi dangane da yadda ya kamata mata musulmi su shiga cikin harkokin zamantakewa a dama da su domin a fahimci addinisu da matsayinsa a cikin rayuwa ta zamantakewa.
412053