IQNA

An Fara Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Jami'o'in Kasashen Musulm

0:05 - May 29, 2009
Lambar Labari: 1784327
Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da taron jami'oin kasashen musulmi a birnin San'a fadar mulkin kasar Yeman da ke samun halartar masana daga kasashen musulmi da ma wadanda ba na musulmi ba.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na yeman online cewa; An fara gudanar da taron jami'oin kasashen musulmi a birnin San'a fadar mulkin kasar Yeman da ke samun halartar masana daga kasashen musulmi da ma wadanda ba na musulmi ba. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shi ne karo na takwas da ake gudanar da irin wannan taro, ba don komai ba sai don a kara kusanto da fahimta tsakanin kasashen musulmi dangane da yadda ya kamata su karbi ci gaban zamani daidai da koyarwar irin ta addinin musulunci tare da yin aiki da wannan ci gaba ba tare da saba wa koyarwar addini ba. Da dama daga cikin masana musamman ma malaman jami'a daga cikinsu sun gabatar da jawabai da makaloli a wajen wannan taro, inda suke bayyana mahangarsu dangane da yadda ya kamata kasashen musulmi su karbi ci gaban zamani.

412026

captcha