IQNA

An Gudanar Da Gasar Karatun Kur'ani A Kasar Iraki

0:03 - May 29, 2009
Lambar Labari: 1784328
Bangaren kasa da kasa: An gudanar da gasar karatun kur'ani ta kasa baki daya a birnin Nasiriya na kasar Iraki, inda daruruwan makaranta kur'ani da daliban jami'a daga sassa daban-daban na kasar Iraki suka samu halartar wannan gasa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Yarana cewa; An gudanar da gasar karatun kur'ani ta kasa baki daya a birnin Nasiriya na kasar Iraki, inda daruruwan makaranta kur'ani da daliban jami'a daga sassa daban-daban na kasar Iraki suka samu halartar wannan gasa. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasa an gudanar da ita ne karkashin kulawar wasu cibiyoyi na addinin musulunci, da ke kula da harkokin kur'ani a fadin kasar Iraki. Bayan kammala gasar an gabatar da laccoci na yin hannuka mai sanda ga matasa, musamman ma wadanda ba su da masaniya kan muhimman abubuwan da suka rataya a kansu a matsayinsu na musulmi, ta yadda hakan zai zama wata matashiya gare su domin yin riko da koyarwar addinin musulunci a cikin dukkanin harkokin rayuwa.

411980


captcha