Bangaren fikra da ilimi; Za a gudanar da wani taro domin nazari kan ilimin falsafa a mahangar marigayi Imam Khomeini(RA) wanda za a gudanar a birnin Napol na kasar Italia.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; Za a gudanar da wani taro domin nazari kan ilimin falsafa a mahangar marigayi Imam Khomeini(RA) wanda za a gudanar a birnin Napol na kasar Italia. Shugaban bangaren kula da al'adu da harkokin ilimi na ofishin jakadancin jamhuriyar musulunci ta Iran Alireza Isama'ili ya bayyana cewa; a wajen wannan taro za a yi bahasi dangane da mahangar Imam kan wasu batutuwa da suka shafi ilmomin falsafa, wanda kuma masana daga sassa daban-daban na kasar Italia za su halarci zaman taron, daga cikinsu kuwa hard a masana a kan ilimi falsafa. Ya ce daga cikin abubuwan da za a yi hard a duba wasu daga cikin littafansa na falsafa domin sanin mahangarsa a kan wasu batutuwa da taron zai yi dubi kansu.
412193