IQNA

Taron Hadin Guiwar Jam'iyun Musulunci A Turkiya

16:25 - May 30, 2009
Lambar Labari: 1785010
Bangaren kasa da kasa: Taron kasa da kasa na hadin guiwar jam'iyun musulunci a Turkiya karo na sha takwas.
Bayan ta nakalto daga ESAM.org.tr cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa; wannan taro ana gudanar da shi ne karkashin kulawar cibiyar bincike da nazarin tattalin arziki da zamantakewar kasar Turkiya ESAM kuma za a ci gaba da gudanar da wannan taro har zuwa gobe .Mahalarta taron na kasa da kasa na hadin guiwar kungiyoyi da jam'iyun musulunci za su yi nazari da bincike ne kan rikicin tattalin arziki da duniyar musulunci ke ciki da kuma rawar da za ta taka wajen warware wannan matsala da ta shafi duniya baki daya.

412761


captcha