Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoto bayan ta nakalto daga jaridar Alshark Ausat ta kasar Masar cewa: wani gungu na masu bincike da nazari musulmai a jami'ar Azzahar a wani zamane da suka gudanar suka dauki wannan mataki cewa Kur'ani mai girma littafi ne na Allah madaukakin sarki kuma fahimtar hakikanin abubuwa da bayanai da ke kumshe a cikin wannan littafi yana bukatar sanin wannan yare da aka sabkar da wannan littafi da shi don haka suka haramta rubuta littafin Alkur'ani da harrufan turancin Ingilishi.
412714