Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya was cewa; Ministocin harkokin tattalin arziki na kasashen musulmi za su gudanar da zamansu har tsawon kanaki uku a jere a birnin Ishqbad fadar mulkin kasar Turkmenestan. Rahoton ya ci gaba da cewa kasashe mambobi a bankin musulunci su ne suka dauki nauyin shirya gudanar da wannan zaman taro, wanda shugaban kasar Turkmenetan zai sanya ido dangane da yadda za a gudanar da taron. Ministocin harkokin tattalin arziki da kudi na kasashen musulmi 56 ne za su halarci wannan taro, tare da manyan daraktoci na bankuna da cibiyoyin kudi 600 daga kasashen musulmi daban-daban.
412830