Bangaren kasa da kasa; Tsohon pira ministan kasar Turkiya Najmuddin Arbakan ya bayyana cewa; Isra'ila ita ce babban ummul haba'isin duk wata matsalar tsaro da ke akwai a mafi yawan kasashen duniya, kuma tana da hannu wajen jefa al'ummomi da dama cikin halin rashin tabbas ta fuskacin tsaro a duniya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na iha.com.tr cewa; Tsohon pira ministan kasar Turkiya Najmuddin Arbakan ya bayyana cewa; Isra'ila ita ce babban ummul haba'isin duk wata matsalar tsaro da ke akwai a mafi yawan kasashen duniya, kuma tana da hannu wajen jefa al'ummomi da dama cikin halin rashin tabbas ta fuskacin tsaro a duniya. Arbakan ya bayyana hakan ne a gaban taron gamayyar kungiyoyin kasashen musulmi, inda ya tabbatar da cewa Isra'ila na hankoron ganin cewa ta aiwatar da shirin nan da take da shi na kafa babbar Isra'ila, wanda kuma ba zai yuwu ba har sai ta hargitsa lamurra ta fuskacin tsaro a wasu kasashe, musamman ma a yankin gabas ta tsakiya, wanda kuma yanzu haka tana hankoron aiwatar da wannan mummunar manufa ne.
412791