IQNA

Za A Gudanar Da Wani Shiri Na Bayar Da Horo Kan Hardar Kur'ani A Kuwait

16:24 - May 30, 2009
Lambar Labari: 1785016
Bangaren kasa da kasa: Daya daga cikin mambobin kwamitin kula da harkokin ilimi na jami'ar Kuwait Abdulmohsen Almutairi, ya bayyana cewa za a gudanar da wani shiri na bayar da horo kan hardar kur'ani mai tsarki a kasar Kuwait, wanda kuma wannan shi ne karo na bakwai da za a gudanar da wannan shiri.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Al-ra'ayi ta kasar Kuwait cewa; Daya daga cikin mambobin kwamitin kula da harkokin ilimi na jami'ar Kuwait Abdulmohsen Almutairi, ya bayyana cewa za a gudanar da wani shiri na bayar da horo kan hardar kur'ani mai tsarki a kasar Kuwait, wanda kuma wannan shi ne karo na bakwai da za a gudanar da wannan shiri. Ya ci gaba da cewa wanna shiri zai hada da mahardata kur'ani na kasar Kuwait da ma wasu da za su zo daga kasashen duniya, kuma shirin na hadin gwiwa ne tsakanin jami'ar Kuwait da kuma kungiyar kula da harkokin addinin musulunci ta duniya. Za a gudanar da shirin ne cikin kwanaki hamsin, kuma akwai kwararrun malaman jami'a da suka kware ta fuskacin bayar da horo kan hardar kur'ani da za su bayar da horon.

412734

captcha