Bangaren kasa da kasa: An gyara tarjamar kur'ani da aka yi da yaren Diyuhi na kasar Maldev, bayan samun wasu kusakurai a cikin tarjamar, kuma a cikin wannan makon ne za a fitar da kur'ani mai sahihiyar tarjama.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Haveeru cewa; An gyara tarjamar kur'ani da aka yi da yaren Diyuhi na kasar Maldev, bayan samun wasu kusakurai a cikin tarjamar, kuma a cikin wannan makon ne za a fitar da kur'ani mai sahihiyar tarjama. A shekarar da ta gabata ce bayan gudanar da bincike dangane da kur'anin da aka tarjama zuwa yaren Diyuhi, wanda kuma shi ne yaren gwamnati a kasar Maldev, an gano wasu kusakurai a cikin tarjamar, lamarin da shugaban kasar ya bayar da umurni da a dakatar da buga wannan kur;ani da aka tarjama, kuma ya umurci dukkanin wadanda suke da shi a hannusu da su mika shi ga wata hukuma ta musamman, domin kaucewa yaduwar kur'ani mai dauke da kuskuren tarjama, ya kuma bayar da umurni da a sake gyara tarjamar domin sake raba shi ga jama'ar kasar.
412747