IQNA

Dalibai 500 Ne Suka Karbi Shedar Kammala Karatun Kur'ani A Turkiya

16:23 - May 30, 2009
Lambar Labari: 1785019
Bangaren kasa da kasa: Dalibai dari biyar ne suka samu takardun shedar kammala samun horon harda da karatun kur'ani a kasar Turkiya, bayan da suka samu horo har na tsawon watanni takwas a jere.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran CIHAN cewa; Dalibai dari biyar ne suka samu takardun shedar kammala samun horon harda da karatun kur'ani a kasar Turkiya, bayan da suka samu horo har na tsawon watanni takwas a jere. Rahoton ya ce an gudanar da bikin bayar da takardun shedar kammala samun horon ga daliban, inda shugaban makarantun koyar da karatun kur'ani na kasa da kuma gwamnan lardin palan doken gami da babban daraktan harkokin ilimi na lardin duk suka halarci bukin bayar da takardun shedar kammala samun horon ga daliban. An sanar da bude wani shafi na internet da daliban za su iya yin amfani da shi wajen ci gaba da karfafa karatu ko hardar kur'ani mai tsarki a duk inda suke.

412744


captcha