IQNA

Ayyukan Imam Khomeini (RA) Ci Gaban Jihadin A'imma (AS) Ne

12:20 - June 01, 2009
Lambar Labari: 1785496
Bangaren kasa da kasa: A cikin irin mawuyacin halin da Imam Khomeini ya samu kansa ya iya kifar da gwamnatin sarki Shah bisa dogaro da Allah madaukakakin sarki, tare da kafa tsarin musulunci a Iran, hakika wannan aiki na Imam ci gaban jihadin a'imma (AS) ne.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Awal cewa; babban sakataren kungiyar Haq ta kasar Bahrain Hassan Moshaimi ya bayyana cewa; A cikin irin mawuyacin halin da Imam Khomeini ya samu kansa ya iya kifar da gwamnatin sarki Shah bisa dogaro da Allah madaukakakin sarki, tare da kafa tsarin musulunci a Iran, hakika wannan aiki na Imam ci gaban jihadin a'imma (AS) ne. Ya bayyana hakan ne jiya a lokacin da ake gudanar da wani zaman taro a birnin Manama fadar mulkin kasar Bahrain, dangane da zagayowar lokacin rasuwar imam Khomeini (RA) inda ya jaddada cewa rayuwar Imam abin koyi ce ga dukkanin musulmi da 'yan adam baki daya, domin kuwa rayuwarsa rayuwa ce ta tsoron Allah, hidima ga jama'a da kuma 'yan adamtaka.

413248

captcha