Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Awal cewa; Babbar kungiyar mabiya addinin kirista ta kasar Bahrain ta sanar cewa mabiya addinin kirista na kasar za su halarci tarukan tunawa da zagayowa da rasuwar Imam Kohmeini da za a gudanar a kasar. Shugaban majami'ar kiristoci ta birnin Manama Akram Ta'ami shi ne ya sanar da hakan a jiya, inda ya bayyana cewa tarukan tunawa da zagayowar rasuwar marigayi Imam Khomeini da za a gudanar a kasar Bahrain a ranakun 3 zuwa 4 ga wata mai kamawa, za su samu halartar mabiya addinin kirista daga sassa daban-daban na kasar, domin a cewarsa Imam Khomeini na kowa da kowa da kowa ne, kuma ya cancanci girmama ta musamman daga dukkanin mutane mabiya addiani da masu fafutukan kare hakkin bil adam da dai dai sauransu.
413194