Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Sharq al-ausat cewa; Haramtacciyar kasar Isra'ila ta dauki tsauraran matakai na hana gudanar da taron kasa da kasa kan masallcin Qods da aka shirya gudanarwa a birnin mai alfarma na tsawon mako guda. Taron wanda aka fara gudanarwa jiya ya samu halartar marubuta dam asana daga kasashen duniya daban-daban, amma jim kadan bayan fara gudanar da taron jami'an tsaron Haramtacciyar kasar Isra'ila a cikin kayan sarki sun kai farmakia wurin tare da watsa taron a birnin Qods mai alfarma. Taron dai yana da dangantaka ne da zaben birnin Qods da aka yi a matsayin babban birnin al'adun larabawa na shekara ta 2009, da kuma fadakar da al'ummomin duniya halin da birnin yake ciki, da kuma barazanar da yake fuskanta daga yahudawan sahyuniya.
413122