Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Kuwait cewa KUNA cewa; Hadakar kungiyoyin musulmi a nahiyar turai ta bayyana matukar gamsuwarta da matakin da gwamnatin kasar Danmark ta dauka na koyar da harshen larabci a makarantu da jami'oin kasar kasar. Hadakar kungiyoyin musulmi na nahiyar turai ta sanar da hakan ne a cikin wani bayani da ta fitar jiya, inda ta bayyana cewa daukar wannan mataki zai kara karfafa dangantaka tsakanin gwamnatin Danmark da ma kasashen musulmi musamman ma larabawa daga cikinsu, da kuma kungiyoyin musulmi da ke nahiyar turai, musamman ma idan aka yi la'akari da rashin jituwar da aka samu tsakanin bangarorin musulmi da na Danmark a lokutan baya.
413023