IQNA

An Fitar Da Littafin Ismah A Mahangar Shi'a Da Sunna

Bangaren fikira: Littafin bincike kan Ismah wato kubuta daga aikata duk wani aikin sabo a mahangar shi'a da sunna, wanda wata marubuciya Fatima Muhakkik ta rubuta, na kan hanyar fitowa nan ba da jimawa ba.
A wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Ikna da wani jami'I a cibiyar gudanar da bincike kan ilmomin addinin musulunci a mahangar mazhabobin sunna da shi'a Ali Ansari Ahamdi, ya bayyana cewa; Littafin bincike kan Ismah wato kubuta daga aikata duk wani aikin sabo a mahangar shi'a da sunna, wanda wata marubuciya Fatima Muhakkik ta rubuta, na kan hanyar fitowa nan ba da jimawa ba. Ya ci gaba da cewa a cikin wannan littafi marubuciyar ta yi amfani da salon rubutu na daidaita fahimta tsakanin dukkanin mabiya mazhabobi daga bangaren shi'a ne ko bangaren sunna, wajen kafa dalilai da dukkanin bangarorin biyu suka yi ammana da su, domin bayyana ma'anar Ismah, da kuma sanin su wane ne ma'asumai, da dalilan da suka tabbatar da hakan.

413188