Bangaren kasa da kasa: Za a gudanar da wani taro kan harkokin kudi a mahangar musulunci da kuma matsalolin tattalin arziki da suka addabi kasashen duniya, gami da hanyoyin da za a bi a warware su, wanda za a gudanar a birnin Alkahira na kasar Masar.
Kamfanin dillancin labaran Ikan ya nakalto daga shafin internet na almuhit cewa; Za a gudanar da wani taro kan harkokin kudi a mahangar musulunci da kuma matsalolin tattalin arziki da suka addabi kasashen duniya, gami da hanyoyin da za a bi a warware su, wanda za a gudanar a birnin Alkahira na kasar Masar. Taron wanda kwamitin kula da harkokin tattalin arziki na jami'oin kasashen musulmi ya shirya gudanarwa, zai samu halartar masana kan harkokin tattalin arziki daga kasashen musulmi, gami da malaman jami'oi daga kasashen musulmi da na larabawa. Inda za su tattauna muhimman batutuwa da suka shafi harkokin tattalin arziki da mahangar musulunci a kan hakan.
413662