Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na arab online cewa; An bude wani baje kolin manyan alluna da ke dauke rubutun kur'ani da aka yi wa ado da nau'oin rubutu daban-daban a kwalejin fasaha da ke jami'ar birnin Haifa da ke arewacin yankunan palastinu da Haramtacciyar kasar Isra'ila ta mamaye. A wannan baje koli an nuna alluna na fasahar rubutun kur'ani a kan manyan alluna da aka yi a palastinu, wanda ya hada da rubutun bakake da salo daban-daban wanda aka kawata tare da nuna hikimar rubutu, wanda kuma dukkanin abubuwan da aka baje suna dauke ne da rubutun kur'ani mai tsarki. Da dama daga cikin mahalarta bikin bude baje kolin da suka fito daga yankuna faban-daban na palastinu sun nuna matukar sha'awarsu kan kayayyakin fasahar da aka nuna a wurin.
413778