IQNA

An Bude Wani Shafin Internet Domin Yada Labaran Addini

16:38 - June 01, 2009
Lambar Labari: 1785978
Bangaren kasa da kasa: An bude wani shafin internet na sadarwa domin yada labaran addinin musulunci mai suna tashar labaran kufah, wanda zai rika watsa shirye-shirye daga kasar Iraki.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na gidan talabijin sautul Irak cewa; An bude wani shafin internet na sadarwa domin yada labaran addinin musulunci mai suna tashar labaran kufah, wanda zai rika watsa shirye-shirye daga kasar Iraki. Bayanin ya ci gaba da ccewa wannan shafi zai mayar da hankali ne wajen kalato labarai da suka danganci lamurra na kur'ani, kama daga labaran gasar kur'ani ko ayyukan da cibiyoyin kur'ani ke gudanarwa a ssasa daban-daban na kasashen musulmi, gami da labarai da suka danganci addinin musulunci da ma sauran labarai da suka shafin yankin gabas ta tsakiya baki daya. Da hakan ya hada da labarai na siyasa da tattalin arziki al'adu zamantakewa da dai sauransu.

413852


captcha