IQNA

Harhada Hadisan Imam Ali (AS) Kokari Ne Hada Kan Musulmi

Bangaren fikira da ilimi: Ayatollah Ozma Jawadi Amuli ya bayyana cewa; kokarin da Sayyid Radi ya yi na hada kalaman Imam Ali (AS) kokari ne na hada kan al'ummar musulmi, inda ya hada littafin Nahjul balaga domin hada kan kan mabiya mazhabar shi'a da sunna.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; A wata ganawa da ya yi da daliban jami'ar Amir Kabir ta birnin Tehran da reshenta da ke birnin Isfahan, Ayatollah Ozma Jawadi Amuli ya bayyana cewa; kokarin da Sayyid Radi ya yi na hada kalaman Imam Ali (AS) kokari ne na hada kan al'ummar musulmi, inda ya hada littafin Nahjul balaga domin hada kan kan mabiya mazhabar shi'a da sunna. Ya ci gaba da cewa idan aka duba sharhin da Sayyid Radi ya yi a cikin littafin Nahjul balaga, za a ga bayanan da ya yi na hadin kai tsakanin al'ummar musulmi musamman ma dai tsakanin sunna da shi'a, inda ya ce shi'a da sunna da sunna 'yan juna ne musulmi. Jawadi Amuli ya ce hada hadisan Imam Ali da Sayyid Radi ya yi ya taimaka matuka wajen hada kan al'ummar musulmi.

413684