Bangaren rahoto: Za a gudanar da wani zaman taro da zai yi dubi kan mahangar Imam Khomeini (RA) dangane da batun palastinu da makomar mamayar yankunan palastinawa da yahudawa ke ci gaba da yi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; Za a gudanar da wani zaman taro da zai yi dubi kan mahangar Imam Khomeini (RA) dangane da batun palastinu da makomar mamayar yankunan palastinawa da yahudawa ke ci gaba da yi. Taron wanda 'yan jami'oi suka shirya gudanarwa a cikin mako mai zuwa, zai yi dubi ne kan irin muhimmancin da Imam ya baiwa batun palastinu da kuma bakar manufar yahudawa ta mamaye palastinu da sauran yankuna masu tsarki da ke cikin yankunan palastinu, musamman ma a birnin Qods mai alfarma. Daga cikin wadanda za su halarci wannan zaman taro da za su gabatar da jawabai akwai mambobin kungiyar Hamas da wasu kungiyoyi na gwagwarmayar palastinawa.
413884