Bangaren manema labarai: ofishin da ke kula da yada al'adun kasar Iran a kasar Sera lanka ya dauki dawainiyar yin karin bayani kan littafin Jihadul Akbar a daidai lokacin tunanawa da rasuwar Imam Khomeini (R) muassasin juyin juya halin musulunci a Iran.
Bayan ta nakalto daga ofishi mai kula da al'adun kasar Iran a wannan kasa ta Sera langa ,cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: a daidai wannan lokaci da ranar rasuwar Muassasin juyin juya halin musulunci a Iran Imam Khomeini (R) za a yi karin bayani ga al'umma a wannan kasa kan littafin Jihadul Akbar da kuma irin abubuwan da ya kumsa masu kima da kuma hanyoyin aiki da su.Kuma wannan aiki za a gudanar da shi ne karkashin hadin guiwar hukumar da ke kula da duk wani abu da marigayi Imam Khomeini (R) ya bari.
413797