IQNA

Za A Gudanar Da Taron Tattalin Arzikin A Musulunci A Palastinu

15:51 - June 02, 2009
Lambar Labari: 1786484
Bangaren kasa da kasa: Za a gudanar da taron tattalin arziki da ayyukan banki a musulunce a dakin gudanar da taruka na babbar cibiyar gudanar da bincike ta jami'ar birnin Khalil da ke gabar yamma da kogin Jordan a Palastinu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Muhit cewa; Za a gudanar da taron tattalin arziki da ayyukan banki a musulunce a dakin gudanar da taruka na babbar cibiyar gudanar da bincike ta jami'ar birnin Khalil da ke gabar yamma da kogin Jordan a Palastinu. An zabi birnin Khalil ne domin gudanar da wannan taro a cikinsa saboda zaben Qods da aka yi a matsayin birnin al'adun larabawa na shekara ta 2009, wanda kuma bankin musulunci ne zai dauki nauyin gudanar da taron baki daya. Masana daga daga sassa daban-daban na kasashen musulmi da na larabawa za su samu halartar wannan taro, domin yin dubi kan matsalolin tattalin arziki da suka addabi duniya da kuma samun hanyoyin da kasashen musulmi za su bi domin warware su a mahanga ta musulunci.


414495



captcha