Bangaren kasa da kasa: Kwamitin raya al'adun musulunci na kasar Kuwait bisa sa idon cibiyar kula d aharkokin addini ta kasar, zai buga kwafin kur'ani mai tsarki har miliyan daya da nufin raba su ga musulmi masu bukata a kasashe daban-daban.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Al-ra'ayi cewa; Kwamitin raya al'adun musulunci na kasar Kuwait bisa sa idon cibiyar kula d aharkokin addini ta kasar, zai buga kwafin kur'ani mai tsarki har miliyan daya da nufin raba su ga musulmi masu bukata a kasashe daban-daban. Shugaban kwamitin Fahad Masir Zufairi ya ce gudanar da wannan aiki zai taimaka wajen kara yada adadin kur'anai da ke akwai yanzu haka a hannun musulmi, yayin da wasu musulmin da suke rayuwa a wasu kasashen ba su da hanyar da za su samu kur'ani domin karantawa. Ya ce yanzu haka dai an shiga aiki buga wadannan kur'anai gadan-gadan, kuma a cewarsa wannan somin tabi ne, daga bisani za a ci gaba da gudanar da wannan aiki na alhairi.
414406