IQNA

An Gudanar Da Gasar Karatun Kur'ani Ta Makafi A Istanbul

15:51 - June 02, 2009
Lambar Labari: 1786487
Bangaren kasa da kasa: An gudanar da wata gasar karatun kur'ani da ta kebanci makafi a birnin Istanbul na kasar Turkiya, wanda cibiyar kula da harkokin makafi ta birnin ce ta dauki nauyin shiryawa tare da gudanar da wannan gasa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran CIHAN cewa; An gudanar da wata gasar karatun kur'ani da ta kebanci makafi a birnin Istanbul na kasar Turkiya, wanda cibiyar kula da harkokin makafi ta birnin ce ta dauki nauyin shiryawa tare da gudanar da wannan gasa. Rahoton ya ci gaba da cewa gasar ta samu halartar makafi makaranta kur'ani mai tsarki, dukkaninsu kuma 'yan kasar Turkiya ne, inda suka yi amfani da kur'ani da aka rubuta da haruffan bril, wato bakaken da makafi ke amfani da su wajen karanta rubutu. Limamin juma'a na yankin Fatih da ke birnin Istanbul na sheikh Abdulsamad Aiden ya bayyana cewa; wannan shi ne karo na farko da aka gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki da ta kebanci makafi a kasar Turkiya, wadda malamai da dama suka bayar da gudunmawarsu domin ganin an gudanar da ita kamar yadda aka shirya.

414309







captcha