Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar alwatan ta kasar Saudiyya cewa; Kwamitin manayan malaman addinin musulunci na jami'ar Azhar da ke birnin Alkahira n akasar Masar, sun bukaci da a dakatar da nuna wani fim da aka shirya domin tozarta addinin musulunci ta hanyar wulakanta wurare masu tsarki da ke kasar. Kwamitin malaman ya yi wannan kira ne a cikin wata wasika da ya aike wa shugaban kasar ta Masar Husni Mubarak, da a ciki suka bayyana cewa an shirya wannan fim din domin wulakanta wurare masu tsarki da ke kasar, a kan haka ya zama wajibi a gagguta dakatar da wannan fim din, kuma yanzu haka an shirya nuna shi a gidan sinima da ke birnin Iskandariyya na kasar, a kan haka suka kirayi Mubarak da ya dakatar da hakan domin samun zaman lafiya a kasar.
414307