IQNA

An Gudanar Da Taro Kan Shahadar Sayyida Zahra (AS) A Labanan

15:50 - June 02, 2009
Lambar Labari: 1786495
Bangaren siyasa da zamantakewa; An gudanar da taro dangane da zagayowar lokacin shahadar sayyida Fatimat Zahra(AS) a yankin Ansariyya da ke kudancin Labanan, wanda ya samu halartar manyan malamai da suka hada da Sheikh Abdulamir Qabalan.
Kamfanin dillancin labaran Ikna reshen kasar Labanan ya habarta cewa; An gudanar da taro dangane da zagayowar lokacin shahadar sayyida Fatimat Zahra(AS) a yankin Ansariyya da ke kudancin Labanan, wanda ya samu halartar manyan malamai da suka hada da Sheikh Abdulamir Qabalan. Taron wanda ya samu halartar manyan malamai da suka hada da alkalan kasar, da kuma mataimakin shugaban majalisar Shi'a ta kasar Sheikh Abdulamir Qabalan, wanda a wajen taron ya bayyana cewa Sayyida Zahra abin koyi ce ga dukkanin mata na duniya a dukkanin bangarorin rayuwarta, kamar yadda ta kasance mace ce da ke bayyana koyarwa irin ta manzon Allah a aikace a cikin dukkanin sassa na rayuwarta.



414396

captcha