IQNA

Imam Khomeini ® A Kullum Yana Karfafa Tunaninsa Na Hadin Kan Musulmi

Bangaren siyasa: Imam Khomeini ® a kullum a jawabai da maganganunsa yana kalubalantar makiya da hana su kutsawa a cikin harkokin musulmi da karfafa hadin kai a tsakanin musulmi.
Hujjatul Islam walmusulumin Said Muhammad Fakihi shugaban hukumar da ke lura da lamura da suka shafi yan jami'a kuma wakilin jagoran juyin juya halin musulunci a Iran a jami'o'I a wata hira da tattaunawa da cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna dangane da manufar Imam Khomeini da kuma koyarwa irin ta kur'ani ya bayyana cewa: imam duk wani tunani nasa da manufa ya aiwatar da ita a aikace ba wai kawai nazaraiya ba kuma babban misalign manufa da mahangarsa kan hadin kai a tsakanin musulmi.

414120