Bangaren ilimi da tunani: an wallafa da yada littafin nazari kan adalci a cikin harshen Albaniyanci day a kumshi nazariyar Imam Khomeini ® da kuma ofishin da ke kula da yada al'adun Iran ya dauki dawainiyar wannan aiki.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran ikna ce ta watsa rahoton cewa; wannan littafi daya daga cikin guraren buga littafi mafi shahara a wannan kasa aka buga shi da kuma ya kumshi mahangar Imam Khomeini mu'assasin juyin juya halin musulunci a Iran a bangarori daban-daban da suka shafi rayuwa da addini da zamantakewar jama'a.Kuma ofishin da ke kula da yada al'adun Iran a wannan kasa ta albaniya ya dauki dawainiyar buga wannan littafi mai kima da daraja.
414391