Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na du'at online cewa; Ministan ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Aljeria Bu Abdullah Golamullah ya bayyana cewa; hana yahudawan sahyuniya ci gaba mamaye Qods wajibi ne na shari'a da ya hau kan musulmi baki daya. Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da wasu masu isar da sakon musulunci da suka hada da limaman masallatai na kasar, inda ya bayyana cewa batun kare wurare masu tsarki da ke cikin palastinu ba wai nauyi ne da ya rataya kan al'ummar palastinu kawai ba, hakan nauyi ne da ya rataya kan dukkanin musulmin duniya. Ya ce dole ne a fadakar da dukkanin musulmi kan nauyin da ya rataya kansu, kuma hakan ya hau kan malamai ne da limamai gami da masu isar da sakonnin addinin musulunci.
415150