Bangaren kasa da kasa: An gudanar da wani zama na musamman kan raya salla a kasar Turkiya, wanda ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar tare da hadin gwiwa da kwamitin kula da harkokin salla na kasar suka shirya gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; An gudanar da wani zama na musamman kan raya salla a kasar Turkiya, wanda ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar tare da hadin gwiwa da kwamitin kula da harkokin salla na kasar suka shirya gudanarwa. Daya daga cikin manyan malaman addini na kasar Muhammad Amin Karatach ya halarci wurin taron, da kuma magajin garin birnin Sin hauran Hassan Lofchali, gami da masana da kuma malaman makarantu da na jami'oin kasar. A lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen taron, Muhammad Amin ya bayyana cewa; salla tana da matsayi na musamman a addinin musulunci, bilhasali ma ita gishiki ce daga cikin gishikan addini.
415107