IQNA

Gwagwarmayar Imam Khomeini (RA) Ta Ginu Kan Koyarwar Kur'ani

19:40 - June 05, 2009
Lambar Labari: 1786814
Bangaren kasa da kasa: Gwagwarmayar Imam Khomeini ta ginu ne kan koyarwa da manufofi na kur'ani mai tsarki, wanda kuma hakan shi ne ya ba shi cikakkiyar nasara da taimakon ubangiji har ya iya jagorantar juyin juya halin islama da ya kai ga kafa tsari na musulunci a Iran.
A cikin wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Ikna da babban sakataren makarantar addinin musulunci ta Rasul a'azam da ke birnin Kano a Nigeria Saleh Muhammad sani ya bayyana cewa: Gwagwarmayar Imam Khomeini ta ginu ne kan koyarwa da manufofi na kur'ani mai tsarki, wanda kuma hakan shi ne ya ba shi cikakkiyar nasara da taimakon ubangiji har ya iya jagorantar juyin juya halin islama da ya kai ga kafa tsari na musulunci a Iran. Ya ci gaba da cewa gwagwarmayar Imam Khomeini na dauke da darussa masu yawa ga musulmi, domin kuwa dogaro da Allah da kuma yin koyi da hakikanin koyarwa irin ta addinin musulunci, da aikata umurnin ubangiji day a zo cikin kur'ani, shi ne sirrin nasarar da ya samu a gwagwarmayarsa da ma rayuwarsa baki daya har ya koma ga ubangiji.

414871





captcha