IQNA

Tawagar Iraniyawa Na Halartar Tattaunawar Addinai A Tunisia

19:44 - June 05, 2009
Lambar Labari: 1786820
Bangaren siyasa da zamantakewa: Tawagar Iran karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Iran Sayyid Muhammad Khatami na halartar taron tattaunawa tsakanin addinai da za a gudanar a kasarTunisia.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; Tawagar jamhuriyar musulunci ta Iran karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Iran Sayyid Muhammad Khatami na halartar taron tattaunawa tsakanin addinai da za a gudanar a kasarTunisia. Ministan kula da harkokin al'adu na kasar Tunisia shi ne ya tarbi tawagar Iran a filin safka da tashin jiragen sama na Tunisia, tare da jakadan kasar Iran da sauran jami'an ofishin jakadancin jamhuriyar musulunci ta Iran da ke kasar. Bayan isar tawagar ta Iran Sayyid Khatami ya gana da Iraniya mazauna kasar a ofishin jakadancin Iran, daga nan kuma ya isa wajen da aka bude taron a fadar shugaban kasa, kafin daga bisani ya wuce zuwa birnin Kirawan, inda za a kammala taron a ranar Alhamis mai zuwa.

415008


captcha