IQNA

An Bude Cibiyar Musulunci A Birnin Amstardam Na Holland

19:43 - June 05, 2009
Lambar Labari: 1787227
Bangaren kasa da kasa: An bude wata babbar cibiyar musulunci a birnin Amstardam na kasar Holland, wanda cibiyar Turkawa mazauna kasar ta dauki nauyin ginawa domin kula da harkokin musulmi musamman ma mazauna birnin.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran CIHAN cewa; An bude wata babbar cibiyar musulunci a birnin Amstardam na kasar Holland, wanda cibiyar Turkawa mazauna kasar ta dauki nauyin ginawa domin kula da harkokin musulmi musamman ma mazauna birnin. Rahoton ya ci gaba da cewa an gina wannan babbar cibiya a gefen babban masallacin birnin Holland wanda mabiya addinin musulunci mazauna birnin suke gudanar da harkokinsu na addini a cikinsa, wanda kuma gina wannan cibiya zai taimaka ma musulmin birnin wajen samun wani wuri na musamman domin gunar da harkokinsu na addini, da hakan ya hada da taruka da dai sauransu. Dan majalisar dokokin kasar musulmi da ke wakilatar Turkawa a majalisar dokokin kasar Mirala ak shi ne ya jagoranci bude cibiyar.

415704
captcha