IQNA

An Yi Kira Ga Musulmi Da Su Yi Koyi Da Kur'ani Wajen Hada Kansu

19:42 - June 05, 2009
Lambar Labari: 1787230
Bangaren kasa da kasa: Wajibi ne musulmi su yi koyi da kur'ani mai tsarki wajen yin aiki da ayoyin da suka wajabta musu hada kai da juna, matukar dai suna son su zama mafifiyar al'umma kamar yadda kur'ani mai tsarki ya siffanta su.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; babban malamain addinin nan na kasar Saudiyya Allmah Sheikh hassan Alhabib ya bayyana cewa; Wajibi ne musulmi su yi koyi da kur'ani mai tsarki wajen yin aiki da ayoyin da suka wajabta musu hada kai da juna, matukar dai suna son su zama mafifiyar al'umma kamar yadda kur'ani mai tsarki ya siffanta su. Sheikhin malamain ya bayyana hakan ne a wajen taron da aka shirya domin yin dubi kan muhimmancin hadin kan alummar musulmi a mahangar Imam Khomeini (RA) inda ya bayyana cewa hakika al'ummar musulmi idan da za ta yi riko da koyarwar kur'ani, tare da yin aiki da ayar da ta wajabta musu hadin kai, da sun zama mafificiyar al'umma kamar yadda kur'ani ya kira su.

415622




captcha