IQNA

Dabi'un Imam (RA) Sun Doru Ne Kan Koyarwar Manzon Allah (SAW)

19:41 - June 05, 2009
Lambar Labari: 1787232
Bangaren kasa da kasa: Imam Khomeini (RA) ya koyi ilimin tafiyar da jama'a masoya da makiya daga koyarwa irin ta addinin musulunci na hakika ne wanda mason Allah (SAW) ya zo da shi kuma ya koyar da musulmi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga wani malamin jami'a na kasar Kuwait Abdulkhalik Abdulhamid yana cewa; Imam Khomeini (RA) ya koyi ilimin tafiyar da jama'a masoya da makiya daga koyarwa irin ta addinin musulunci na hakika ne wanda mason Allah (SAW) ya zo da shi kuma ya koyar da musulmi. Ya ci gaba da cewa idan muka kalli tarihin manzon Allah da yadda ya zauna da munakai da masoya na gaskiya, da yadda ya nuna kyawan dabi'u nay an adamtaka wajen tafiyar da kowa, da kuma yadda Imam Ali (AS) ya tafiyar da munafukai da ya zauna tare da su da hakan ya hada khawarijawa, za mu ga cewa Imam Khomeini yana yin koyi ne da irin wannan tafarki da tarbiya.

415455


captcha