IQNA

An Gudanar Da Gasar Karatun Kur'ani A Karachai-Charkisia

22:19 - June 06, 2009
Lambar Labari: 1787846
Bangaren kasa da kasa: An gudanar da gasar karatun kur'ani a jamhuriyar Karachai-Charkisia, wanda jami'ar musulunci ta birnin Ust Cogete ta shirya gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Dunya Bulteni cewa; An gudanar da gasar karatun kur'ani a jamhuriyar Karachai-Charkisia, wanda jami'ar musulunci ta birnin Ust Cogete ta shirya gudanarwa. Rahoton ya ci gaba da cewa makaranta kur'ani da dama daga sassa daban-daban na kasar sun halarci wannan gasar karatun kur'ani, kamar yadda wasu daga cikin jami'an gwamnati da suka hada da magajin garin birnin Ust Cogete Rasul Comeav da wasu daga cikin malaman addinin musulunci na jamhuriyar duk sun halarci wannan gasar karatun kur'ani. Jamhuriyar Karachai-Charkisia daya ce daga kasashen tarayyar Soviet.

416378
captcha