Bangaren kasa da kasa: Za a gudanar da wata zanga-zangar nuna kin jinin yahudawan sahyuniya a birnin Washington na kasar Amurka, wanda kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasar suka shirya gudanarwa a ranar Asabar a gaban ofishin jakadancin Isra'ila da ke birnin domin nuna goyon baya ga al'ummar palastinu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran sana cewa; Za a gudanar da wata zanga-zangar nuna kin jinin yahudawan sahyuniya a birnin Washington na kasar Amurka, wanda kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasar suka shirya gudanarwa a ranar Asabar a gaban ofishin jakadancin Isra'ila da ke birnin domin nuna goyon baya ga al'ummar palastinu. Rahoton ya ci gaba da cewa wadanda za su gudanar da wannan zanga-zanga wadanda dukkaninsu sun fit one daga kungiyoyin kare hakkin biladama na kasar, sun jaddada wajabcin kawo karshen killacewar da Isra'ila ke ci gaba da yi wa al'ummar Gaza bisa zalunci.
416303