Bangaren kasa da kasa: Za a fara gudanar da wani shiri na bayar da horo ga musulmi kan karatun kur'ani da hadisi a jahar Carolina ta kasar Amurka, wanda cibiyar kula da harkokin addinin musulunci ta jahar ta shirya gudanarwa a kowane mako daga gobe.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na cibiyar musulunci ta Rali cewa; Za a fara gudanar da wani shiri na bayar da horo ga musulmi kan karatun kur'ani da hadisi a jahar Carolina ta kasar Amurka, wanda cibiyar kula da harkokin addinin musulunci ta jahar ta shirya gudanarwa a kowane mako daga gobe. Bayanin ya ci gaba da cewa za a ci gaba da gudanar da wannan shiri har zuwa watan Ramadan mai zuwa, daga cikin abin da shirin zai kunsa kuwa hard a bayar da fatawa kan mas'aloli daban-daban na addinin musulunci, da kuma yadda ya kamata musulmi ya yi riko da koyarwa irin ta addininsa, haka nan kuma za a rika gabatar da laccoci na addini.
416333