Bangaren kasa da kasa: An gudanar da taron tunawa da cika shekaro ashirin da rasuwar marigayi Imam Khomeini (RA) a jami'ar birnin Dakar fadar mulkin kasar Senegal, wanda ya samu halartar masana da malaman jami'a daga sassa daban-daban na kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran lesoleil cewa; An gudanar da taron tunawa da cika shekaro ashirin da rasuwar marigayi Imam Khomeini (RA) a jami'ar birnin Dakar fadar mulkin kasar Senegal, wanda ya samu halartar masana da malaman jami'a daga sassa daban-daban na kasar. Taron wanda aka gudanar a babban dakin gabatar da taruka na jami'ar birnin Dakar na Senegal, ya samu halartar wakilan cibiyoyi na addini da kuma jami'an huldar deplomasiyya na kasar Iran da ke birnin, daga ciki kuwa harda jakadan jamhuriyar musulunci ta Iran, gami da wasu malaman addini. An gabatar da jawabai da dama, da ke yin kira ga al'ummar musulmi da su yi koyi da Imam Khomeini a cikin dukkanin ayyukansa da gabatar a cikin rayuwarsa, wandda hakan ke tattare da izzar musulmi da kuma daukakarsu.
416339