IQNA

Mabanbantan Ra'ayoyi Dangane Da Jawabin Barack Obama

22:16 - June 06, 2009
Lambar Labari: 1787855
Bangaren kasa da kasa: Tun bayan da shugaban kasar Amurka Barack Obama ya gabatar da jawabinsa kwanaki biyu da suka gabata ga duniyar musulmi a birnin Alkahira na kasar Masar, al'ummomin duniya da suka hada da musulmi suke ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan wannan jawabi da kuma manufarsa gami da abin da ya kunsa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Faransa AFP cewa; Tun bayan da shugaban kasar Amurka Barack Obama ya gabatar da jawabinsa kwanaki biyu da suka gabata ga duniyar musulmi a birnin Alkahira na kasar Masar, al'ummomin duniya da suka hada da musulmi suke ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan wannan jawabi da kuma manufarsa gami da abin da ya kunsa. A nata bangaren kungiyar kula da harkokin ilimi da al'adu ta kasashen musulmi ISESCO ta bayyana cewa akwai canji a cikin irin kalaman da aka saba ji daga bakunan shugabannin Amurka, yayin da wasu kuma suke ganin cewa akwai karo da juna tsakanin kalaman Obama da kuma abin da Amurka take yi a aikace.

416372




captcha