IQNA

Za A Gudanar Da Taron Girmama Mahardata Kur'ani A Turkiya

22:15 - June 06, 2009
Lambar Labari: 1787856
Bangaren kasa da kasa: Za a gudanar da wani taron girmama mahardata kur'ani tare da ba su takardun shekadar kammala hardar kur'ani mai tsarki a birni uskudar na kasar Turkiya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga daga kamfanin dillancin labaran Yeni Asya cewa; Za a gudanar da wani taron girmama mahardata kur'ani tare da ba su takardun shekadar kammala hardar kur'ani mai tsarki a birni uskudar na kasar Turkiya. Bayanin ya ci gaba da cewa babban limamin masallacin juma'a na birnin shi ne babban bako da zai jagoranci mika takardun shedar kammala hardar kur'anin ga mahardatan da za su halarci wurin taron.Daya daga cikin wadanda suka shirya gudanar da wannan taro karkashin cibiyar kula da harkokin addini musulunci ta birnin ya bayyana cewa, manufar hakan ita ce karfafa gwiwar mahardatan domin ci gaba da bayar da himma wajen hardar.

416250
captcha