Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran CIHAN cewa; Za a fara gudanar da wani shiri na bayar da horon kan karatun kur'ani da kuma hardarsa amma a lokutan bazaar a kasar Turkiya. Bayanin ya ci gaba da cewa babban malamin nan na birnin Anamur Muhammad Kuchak ya bayyana cewa, wannan shirin zai haifar dad a mai ido matuka matukar dai aka aiwatar da shi kamar yadda aka shirya, domin kuwa akwai dubban matasa da suke shirye su shiga cikin shirin, wanda kuma a cikin lokutan bazaar za su damar koyo ko hardace wani bangare na kur'ani mai girma. Ya kara da cewa za a gudanar da shirin bayar da horon a masallatai kimanin 96 a sassa daban-daban na kasar.
416673