IQNA

Azhar Ba Ta Amince Da Kafa Kwalejin Kur'ani Ta Mata Ba

16:11 - June 07, 2009
Lambar Labari: 1788202
Bangaren kasa da kasa: Shugaban jami'ar musulunci ta Al-azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar Ahmad Tayyib, ya mayar da martani dangane da batun kafa kwalejin kur'ani da kebanci mata kawai, inda ya ce hakan ba za ta sabu ba.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Al-raya ta kasar Qatar cewa; Shugaban jami'ar musulunci ta Al-azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar Ahmad Tayyib, ya mayar da martani dangane da batun kafa kwalejin kur'ani da kebanci mata kawai, inda ya ce hakan ba za ta sabu ba. Mataimakin shugaban kwamitin gudanar da binciken ilimi da nazari na jami'ar Azhar Atiyya Qayyumi ya bayyana cewa; sun yi tattaki musamman zuwa wajen shugaban jami'ar tare da wsu 'yan majalisar dokokin kasar 17 domin mika masa takardar neman kafa wani kwaleji na mata domin koyar da su ilmomin kur'ani mai girma, amma ba a je ko'ina ba mayar da martani kan hakan, tare da nuna rashin gamsuwarsa da duk wani batu makamancin hakan.

416641








captcha