IQNA

Imam Khomeini Rana Ce Da Ta Bullo Daga Gabas Domin Haskaka Duniya

16:13 - June 07, 2009
Lambar Labari: 1788203
Bangaren kasa da kasa: Imam Khomeini rana ce da ta bullo daga gabas kuma ta haskaka duniya da hasken imani da tsoron Allah, da amana da gaskiya da sadaukantarwa, kuma bisa hakan ne haskensa ya wanzu yana ci gaba da haskaka duniya.
A cikin wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Ikna da wani dalibin bangaren nazarin harshe day a fito daga kasar Tajikistan Muhyiddin Sulainuv ya bayyana cewa; Imam Khomeini rana ce da ta bullo daga gabas kuma ta haskaka duniya da hasken imani da tsoron Allah, da amana da gaskiya da sadaukantarwa, kuma bisa hakan ne haskensa ya wanzu yana ci gaba da haskaka duniya. Ya ci gaba da cewa dukkanin rayuwar Imam Khomeini tana cike ne da abubuwan koyi, hakan kuma bai kebance kowa ba, domin kuwa mutumin gari zai iya yin koyi da Imam, kamar yadda shugaba ko jami'I zai iya yin koyi da shi wajen tafiyar harkokin jama'a bisa adalci da tsoron Allah da yin gaskiya gami da rukon amanar al'umma. Ya ce Imam Khomeini ya jawo wa musulunci daukaka a fadin duniya samakon tsarkake niya da yin aiki domin Allah.


416551




captcha